Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar ‘yan sanda ta sanar da kama wasu ‘yan kasashen waje da ke daukar nauyin masu zanga-zanga suna daga tutar kasar Rasha a Kano. Bayanai sun fito.
Wasu 'yan daba a jihar Rivers sun yi yunkurin kawo cikas kan zanga-zangar da ake yi a kan tsadar rayuwa a kasar nan. Sun bugi wasu masu zanga-zanga.
Daga cikin matasa akalla guda biyar da iyalansu su ka tabbatar da rasuwarsu ta hanyar harbi yayin zanga-zanga, hudu daga cikinsu masu karancin shekaru ne.
Gwamnatin tarayya ta yi martani ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar bayan shawartar jami'an tsaro da su dai na harbin masu gudanar da zanga-zanga.
Wasu daga cikin matasan da ke jagorantar zanga-zangar nuna adawa da halin kuncin da ake ciki a Najeriya sun fada hannun jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS).
Rundunar 'yan sanda ta ce ta gano daga inda masu zanga-zanga ke samun tallafin kudi. Sufeta Janar na rundunar ya tabbatar da cewa ba su yi harbi da bindiga ba.
'Yan Najeriya na ci gaba da tururuwa zuwa kan tituna domin nuna adawarsu kan halin kunci da tsadar rayuwar da aka samu a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Rundunar sanda a jihar Kano ta kama wani barawo da ya sace makudan kudi har N15m a karamar hukumar Kunci yayin da yake kokarin guduwa a jihar Katsina.
Gwamnatin Kano ta ce ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanya a fadin jihar. Gwamnatin jihar ya ce yanzu dokar za ta fara aiki 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari