Hukumar yan sandan NAjeriya
Wani sufetan 'yan sanda mai suna Aminu Yahaya Bidda da ke aiki a Kaduna ya shiga matsala bayan da aka kama shi a bidiyo yana cin zarafin ma'aikacin KAEDCO.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yiwa jami'an tsaro kwanton bauna a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun yi garkuwa da wani jami'in dan sanda a yayin harin.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar nan na bukatar akalla alburusai miliyan 350 domin gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci a duk shekara.
Rundunar yan sanda ta kama wani dattijo mai shekaru 60 yana hada kudin ganye, mutumin ya fito daga jihar Filato ne zuwa Bauchi a motar haya inda ya hada kudin.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Salman Garba Dogo, ya bukaci jami'an 'yan sandan da aka yiwa karin girma su jajirce wajen kawar da laifuka a jihar.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi. 'Yan bindigan sun hallaka wani babban basarake yayin harin.
Matafiya sun yi kicibis mugun gamo da 'yan ta'adda hanyar Gusau-Funtua, inda miyagun su ka ɗauke fasinjojin mota uku,tare da sace wasu a Unguwar Chida.
Gwamnatin Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Umar Namadi, ta cire dokar hana fita da ta sanya a kananan hukumomi takwas saboda rikici yayin zanga-zanga.
Wasu mutane sun kama wani mutum mai suna Musa dauke da kan wata mata a cikin buhu, ya ce yana sayar da sassan jikin dan Adam yayin da ake masa tambayoyi.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari