Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar 'yan sanda ta yi ram da wani karamin yaro dan shekara 17, Amir, wanda ake zargi da caka wamatar aure wuka har lahira a Maidugurin jihar Borno.
Wasu jami'an 'yan sanda da sojoji sun ba hamata iska a jihar Filato. Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa ta dauki mataki tare da hukunta masu laifi.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za a kama duk wani jami’in dan sanda da aka gano yana ba babban mutum kariya, bisa umarnin sufetan 'yan sanda, Egbetokun.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dauki matakai domin dakile hare-haren 'yan bindiga. Ya bukaci hadin kan jama'a.
A labarin nan, za a ji cew agwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tabbatar da cewa babu inda aka dakatar da dokar hana acaba a Kano, ta roki jama'a game da kare rayuka.
Yan sandan babban binrin tarayya sun kashe ’yan bindiga uku, sun kama babban dan ta'adda, kuma sun dakile mugun shirin garkuwa da mutane a Abuja.
Kungiyar yan jarida IPI Nigeria ta bayyana laififfukan da wasu gwamnoni suka yi wanda ya sa ta sanya su a jerin wadanda ba su mutunta yan jarida.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da manoman da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Kaduna. Sun tafi da su zuwa cikin daji.
Uban amaryar da aka yi garkuwa da ita a kauyen Chacho na jihar Sakkwato, Malam Umaru ya bayyana cewa masu garkuwa sun kira waya, sun nemi magana da dagaci.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari