Hukumar yan sandan NAjeriya
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nuna goyon bayansa ga batun kafa 'yan sandan jihohi. Ya ce za su taimaka wajen samar da tsaro ga al'umma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani matashi ya rasa rayuwarsa a rikicik da ya biyo bayan zaben fitar da gwanin APC a mazabar Sabon Gari da ke Kaduna.
Wani matashi da ke yin bautar kasa ya shiga hannun ‘yan sanda bayan zarginsa da kashe mahaifinsa, fitaccen ɗan kasuwa Adimike Godwin, bayan gardama kan kuɗi a Abuja.
Kungiyar ITOON ta kai korafi ga ‘yan sanda da DSS kan abin da ta kira cin zarafin Musulmi da kalaman kiyayya a kafafen sada zumunta wanda ya ke neman ta da rigima.
Rahotanni daga yankin gundumar Guga da ke cikin karamar hukumar Bakori sun nuna cewa waus mahara sun kashe akalla mutane 10 a kauyuka 2 ranar Lahadi.
A labarin nan, za a ji cewa zanga-zangar lumana da wasu matasan jihar Kano suka shirya game da matsalar tsaro ta bar baya da kura inda aka yi kone-kone.
'Yan ta'adda sun kai hari a wata makarantar da ake horar da jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Yobe. 'Yan ta'addan sun kashe jami'an 'yan sanda.
‘Yan sandan Katsina sun kama wani mutumi a Babban Asibitin Funtua bisa zargin yunkurin satar mahaifar sabon jariri domin amfani da ita wajen tsafi.
Da safiya yau Juma'a, wasu yan bindiga suka kutsa makarantar sakandire a jihar Oyo, inda suka sace shugabar makarantar da dalibai da yawa da ba a tantance ba.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari