Rashawa a Najeriya
A labarin nan, za a ji yadda kungiyar SERAP ta bukaci gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso a kan ya yi bayani a kan bacewar N3trn daga bankin.
Yan majalisa 12 a Ondo sun fara shirin tsige kakakin majalisar jihar, Olamide Oladiji bisa zargin rashawa, karkatar da N50m da sabawa kundin tsarin mulki.
EFCC ta ayyana tsohon ministan man fetur kuma tsohon Gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin karkatar da dala miliyan 14.8.
EFCC ta mayar wa wata tsohuwa mai shekara 70, Margret Taye Odofin, N42.5m da jami’ar banki ta sace mata, bayan shekara da dama tana neman adalci.
A labarin nan, za a ji cewa wata kotun Amurka ta tabbatar da cewa tsohon Manajan Darakta a kamfanin mai na Najeriya, Paulinus Okoronkwo ya karbi cin hanci.
Lauya mai kare Abba Kyari ya ce babbar kotun tarayya ta wanke dan sanda, Abba Kyari daga karbar kudi daga wajen dan damfara, Hushpuppi da aka rike a Amurka.
Daya daga cikin jaororin APGA na kasa, Cif Chekwas Okori ya caccaki wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyun adawa da ke gudu wa zuwa jam'iyya mai mulki.
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya yi gargadi da cewa cin hanci da rashawa babban laifi ne da zai jawo hana mutum biza komin girmansa a Najeriya.
ICPC ta titsiye dan majalisar jihar Filato, Adamu Aliyu, bisa zargin damfarar dan dan kasuwa N73.6m, a wata kongilar jami’ar Jos, ta bogi, amma ya musanta zargin.
Rashawa a Najeriya
Samu kari