Kasafin Kudi
Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da gina sabuwar kasuwar zamani a Gusau kan Naira biliyan 3.6. An ce za a kammala aikin a cikin watanni 12 bayan ba da kwangilar.
A wannan labarin, za ku ji cewa majalisar dokokin jihar kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika mata domin amincewa.
Kwamishinan muhalli na jihar Sokoto, Nura Shehu Tangaza ya nuna cewa akwai gyara a maganar Gwamna Ahmad Aliyu kan kashe N1.12bn a gyaran rijiyoyin burtsatse./
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin rufe dukkanin asusun banki na hukumomi da ma'aikatun jihar a shirye-shiryen komawa amfani da asusun bai daya.
Gwamnatin Najeriya ta ce ana kashe Naira 120 domin samar da kilowatt 1 na wutar lantarki a kowacce awa. Ta kuma fadi shirinta na kara kudin wutar.
Ana raba ayyukan mazabu ga yan majalisun kasar nan 109 domin gudanar da ayyukan ci gaba a sassa daban-daban na mazabunsu ciki har da Barau Jibrin da Ali Ndume.
Wani sabon rahoto da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta wallafa ya nuna raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya zuwa kashi 33.40 a watan Yulin 2024.
Gwamnatin Kano ta aiwatar da wasu ayyuka guda biyar wadanda suka lakume Naira miliyan 700 a wani yunkuri na samar da tsaftataccen ruwan sha a sassan jihar.
An samu labarin yadda aka raba Naira Biliyan 438 tsakanin Gwamnoni 34 da Ministan Abuja, Nyesom Wike. Zamfara ta samu N49bn amma ba a ba Kaduna ko sisi ba
Kasafin Kudi
Samu kari