Jihar Niger
'Yan bindiga sun kuma kai hari kan dakarun sojoji inda akalla biyu suka samu munanan raunuka a karamar hukumar Rafi da ke jihar Niger a jiya Litinin.
Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da mataimakiyar shugabar matan jam'iyyar ta jihar Neja, Sayyada Amina Shehu na tsawon watanni shida masu zuwa.
Allah ya yiwa wata Hajiya 'yar Najeriya a birnin Madina yayin gudanar da aikin Hajji. Hajiyar wacce ta fito daga Neja ta rasu ne bayan ta kamu da rashin lafiya.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan karamar hukumar Shiroro cikin jihar Neja. Sun hallaka mutum bakwai har lahira.
Majalisar dattawa ta Najeriya za ta gudanar da bincike kan mutuwar da wasu masu hakar ma'adanai suka yi a jihar Neja, bayan dutse ya zaftaro musu.
Wasu mutane da ke tserewa harin 'yan bindiga a jihar Neja sun rasa rayukansu a cikin ruwa. Mutanen sun rasu ne bayan kwale-kwalen da suke ciki ya yi hatsari.
Mutane shida ne ake da tabbacin ceto su daga karkashin baraguzan mahakar ma’adanai a jihar Niger bayan ruftawarsa a makon nan yayin da har yanzu wasu suka makale.
Gwamnatin jihar Niger ta dora laifin gaza ceto wadanda suka makale a karkashin mahakar ma'adanai kan rashin tsaro da ya addabi yankin Galadima-Kogo.
Wasu yan ta'adda sun shiga kauyuka biyu a kananan hukumomin Nunya da Tunga, sun yi awon gaba da Bayin Allah akalla 56 a jihar Neja cikin kwanaki biyu.
Jihar Niger
Samu kari