Jihar Niger
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a jihar Neja inda suka tafka ta'asa. Miyagun sun hallaka 'yan sa-kai tare da yin awon gaba da mutane da dama.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya nemi a kafa sansanonin soja a iyakokin jihar Neja domin hana 'yan bindiga shiga jihar. Ya ce zai ba da matasa 25,000 su shiga soja.
Fadar shugaban kasa ta ce rikicin Arewa ta Tsakiya ya samo asali daga mallakar ƙasa, ta’addanci da satar ma’adinai, yayin da Tinubu ke ƙarfafa zaman lafiya.
Majalisar Wakilai ta yi Allah-wadai da harin da ’yan bindiga suka kai wa konboyin dan majalisa Jafaru Mohammed Ali a Neja, inda jami’an tsaro suka mutu.
Dan majalisar tarayya Jafaru Mohammad Ali Damisa ya tsira daga harin 'yan ta'adda da suka kai wa tawagarsa a hanyar Lumma–Babanna, Borgu, jihar Niger.
Rundunar ’yan sandan Jihar Niger ta kama mutane huɗu da ake zargi da kai hari kan ayarin motocin Gwamna Mohammed Umaru Bago a Bida, bayan zaben ƙananan hukumomi.
Hukumar zaben jihar Neja ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar, jam'iyyar APC ta lashe duka kujerun ciyamomi 25.
Jam'iyyun adawa sun nuna rashin amincewarsu da zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Neja. Sun yi zargin cewa an tafka gagarumin magudin zabe.
Wata kungiyar masu kare hakkin dan adam ta bukaci hukumomi su gaggauta sakin Abubakar Isah Mokwa, dalibin da aka kama kam rubutun da ya yi a Facebook
Jihar Niger
Samu kari