Jihar Niger
Matashin malamin Musulunci daga Jihar Niger ya yi magana bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, yana mai cewa dukkan malamai daya suke wajen kuskuren tafarki.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun yi awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba bayan sun kai wani harin ta'addanci a Neja.
A labarin nan, za a ji cewa Shugaban majalisar dokokin Neja, Rt. Hon. Abdulmalik Sarkindaji ya yi barazana ga gwamnati a kan jan kafa wajen ceto daliban Papiri.
Shugaban CAN na Arewa, Rabaran John Hayab, ya ce wani uba mai yara uku da aka sace a makarantar St Mary’s a Niger, ya mutu sakamakon bugun zuciya.
Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarni a tsaurara tsaro tare da kakkabe 'yan ta'adda a dazuzzukan Kwara, Neja da Kebbi bayan yawaitar sace dalibai da masu ibada.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana dalilin da ya sa sojoji ba za su iya yi wa 'yan bindiga rubdugu ba.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar yan sandan jihar Legas ta sanar da cewa ta kammala shirin tunkarar duk wata barazana da za ta iya kunno kai.
An rufe makarantu da dama da ke a kan iyakar Abuja da jihar Niger saboda matsalar tsaro bayan sace dalibai a Niger da Kebbi. Malamai sun ce matakin na kariya ne.
Kungiyar Katolika ta Kwantagora ta saki sunayen duka malamai da daliban sakandireda, firamare da nazire da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Neja.
Jihar Niger
Samu kari