Nadin Sarauta
Mai Martaba Sarkin Daura ya nada mai dakin Malam Dikko Radda a matsayin Jagaban Matan Kasar Hausa, ta zama ta farko da aka ba wannan sarauta a tarihi.
Gwamna Dikko Radda ya halarci jana'izar diyar sarkin Katsina, Khadijah Abdulmumin Kabir Usman, wacce ta rasu a Abuja. An ce Khadija ta rasu ta bar 'ya'ya uku.
Lamari ya fara daukan zafi a jihar Osun bayan kama Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede. Mutanen yankin sun bukaci a sauya Sarkin da gaggawa bayan daure shi.
Rahotanni daga masarautar Ipetumodu ta nuna cewa an fara duba yiwuwar tube rawanin Sarki bayan kotun Amurka ta daure shi na tsawon watanni 56 a gidan yari.
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya amince da da naɗin Sanusi Mikailu a matsayin sabon sarkin Zuru, don ya gaji marigayi Muhammadu Sani Sami Gomo II.
Sarkin Irokun, Oba Buari Ola Balogun da ke jihar Ogun ya bukaci gwamnatin Ondo ta daina yunƙurin da ya kira ba bisa ka’ida ba na naɗa sabon Sarki a yankin jihar.
Sarkin Iwo da ke jihar Osun a Kudu maso Yamma a Najeriya, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi Allah wadai da masu yada jita-jitar cewa yana shan tabar wiwi.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke na iya tsige mai martaba Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede bayan kotun Amurka ta daure shi na tsawon shekaru.
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya amince da kirkiro karin sarakuna uku domin karfafa ayyukan masarautun gargajiya a jihar Kogi, ya dawo da sarkin Omala.
Nadin Sarauta
Samu kari