Nadin Sarauta
Gwamna Makinde ya nada Yarima Owoade sabon Alaafin na Oyo, yayin da masu nadin sarauta suka kalubalanci nadin bisa hujjar shari’ar da ke gudana a kotu.
Bayan Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan rikicin masarauta, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan hukuncin inda ya ja kunnen al'umma.
Masu nadin sarauta a jihar Oyo sun kalubalanci Gwamna Seyi Makinde kan nadin sabon Alaafin inda suka kalubalance shi kan rashin bin ka'ida da tsari.
Sarkin Lokoja, Alhaji Ibrahim Kabir Maikarfi IV, ya yabawa Gwamna Usman Ododo inda bukaci gwamnati ta bai wa sarakuna mukamai saboda kusancinsu da al'umma.
Masarautar Ilorin ta musanta rahoton da aka fara yaɗawa cewa sarki Sulu Gambari da Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara sun fara zaman doya da manja.
Gwamnan jihar Cross Rivers ya sanar da dakatar da sarki a Esuk Utan bayan korafe korafe an nada kwamitin da zai lura da masarautar har a kammala bincike.
Sarakunan gargajiya daga Kudancin Najeriya sun yi kira ga gwamnati ta magance matsalolin tattalin arziki, sun kuma yi hasashen kyakkyawar makoma ga Najeriya a 2025.
Wani basarake a jihar Osun, Oba Jelili Olaiya ya bayyana cewa gaban 'yan sanda 'yan daba suka masa jina jina tare da matarsa da wasu 'yan fadarsa kan limanci.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya nada Sani Ahmadu Ribadu, wanda ya kasance kani ne ga Malam Nuhu Ribadu, matsayin sabon Sarkin Fufore.
Nadin Sarauta
Samu kari