Nadin Sarauta
Sarkin Beni da ke ƙaramar hukumar Shira a Bauchi, basarake mafi daɗewa a kan sarauta, Muhammadu Inuwa ya riga mu gidan gaskiya a asibitin FMC a Azare.
Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya rushe wasu sababbin masarautu da tsohon gwamna, Godwin Obaseki ya samar inda ya dawowa Oba na Benin, Oba Ewuare II martabarsa.
Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya gwangwaje gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris da sarautar gwarzon daular Usmanuyya saboda taimakon jama'a.
Kotun majistare da ke Ibadan a jihar Oyo ta tsare wasu mutane hudu kan neman bata sunan sarkin Ogbomoso da suke zargin yana neman haddasa fadan addini.
Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya yi zancen da zai batawa wasu malaman addini rai. Dutsen Tanshi ya soki malaman da suka karbi sarautar Sarkin Musulmi
Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ya yabawa dansa, DSP Aminu Lamido Sanusi inda ya fadi musabbabin zabensa a matsayin Chiroman Kano a yau Juma'a.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya shirya bikin nada babban dansa, DSP Aminu Lamido Sanusi sarautar Chiroman Kano a ranar Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024.
Za a ji wanda a shekarun baya can a 1980s aka daure a kurkukun Amurka ya samu sarauta a Najeriya. Shekaru kusan 30 da suka wuce aka same shi da laifin sata a Amurka.
Rikicin manyan APC a Sokoto ya fara raba kan sarakunan gargajiya a jihar Sokoto. Sarakuna sun fara ajiye aiki suna goyon bayan ɓangaren yan siyasa.
Nadin Sarauta
Samu kari