Nadin Sarauta
Masarautar Zazzau ta yi rashin jigo a cikinta, Sarkin Yakin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate wanda ya koma ga mahaliccinsa a safiyar ranar Alhamis.
Babbar kotun jihar Ogun ta soke naɗin basaraken Ilawo, ta ce Gwamna Dapo Abiodun ya rainata da ya ci gaba da harkokin naɗa sarkin duk da an shigar da ƙara.
Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya jaddada ikonsa a mataayin gwamna inda ya gargadi masu neman kawo masa cikas a cikin mulkinsa da cewa su yi hakuri.
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan shari'ar Musulunci a yankin Kudu maso Yamma, Sarkin Ado-Ekiti, Oba Adeyemo Adejugbe, ya rusa kwamitin Shari’a a Masallacin Juma’a.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara Bauchi domin halartar babban taro inda ya nuna godiya ga Sarkin Bauchi da majalisarsa kan addu'o'i.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya tabbatar da bin doka inda ya mayar da basarake, Jonathan Paragua Zamuna matsayin sarkin Piriga bayan Nasir El-Rufai ya tube shi.
Masu zaben sarki a jihar Oyo sun gindaya wa'adin kwanaki 30 ga Gwamna Seyi Makinde ya soke naɗin sabon Alaafin, sun ce ba shi da hurumi a wannan al'amarin.
Hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa a Najeriya watau EFCC ta fara titsiye sarakunan da ke zaben sabon Alaafin na Oyo kan zargin karɓar rashawa.
Gwamnatin Abia ta amince da karin albashi ga sarakunan gargajiya, sake fasalin gudanarwarsu da kuma daukar matakan dakile tuki a hanyar da ba ta dace ba.
Nadin Sarauta
Samu kari