Nadin Sarauta
An tabbatar da rasuwar Sarkin Badagary da je jihar Legas, Mai Martaba De Wheno Aholu Menu-Toyi I, Akran na Badagry, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Sarkin Kagarko a jihar Kaduna, Alhaji Sa’ad Abubakar, bayan fama da jinya, inda ya rasu a yau Alhamis 8 ga watan Janairun 2026.
Gwamnatin jihar Bauchi ta bukaci sababbin hakiman da su maida hankali wajen inganta rayuwar jama'ar da suke jagoranta, tuni aka raba masu takardun fara aiki.
Ana zargin ministan FCT, Nyesom Wike da rashin girmama sarakuna da masu fada a ji a birnin tarayya Abuja. Kungiyar 'yan asalin Abuja, AOIYEO ce ta yi zargin.
‘Yan bindiga sun kai hari inda suka sace Sarkin Aafin, Oba Simeon Olaonipekun, tare da ɗansa Olaolu bayan kai farmaki fadar sa a Ifelodun, Jihar Kwara.
An shiga jimami a jihar Enugu bayan rasuwar babban basaraken gargajiya, Mai Martaba, Igwe PD Uzochukwu, kwana guda kafin cikar sa shekara 90 a duniya.
Fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa zai bude fadar Sarkin Wakar Kasar Hausa tare da nada hakimai da sauran masu taimaka wa sarki.
Mai martaba Alaafin na jihar Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade, ya shirya nada 'dan shugaban kasa, Seyi Tinubu a sarautar Okanlomo na Ƙasar Yarbawa.
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da majalisar masarautun Katsina domin karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da sarakuna kan tsaro.
Nadin Sarauta
Samu kari