Musulmai
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya yi jimami bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci na Ilorin, Sheikh Hamzah Ariyibi, wanda ya yi fice.
Kakakin rundunar yan sanda a jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya musanta rahoton sace masallata 40 inda ya tabbatar da cewa mutane takwas kawai aka dauke a jihar.
Izala ta Najeriya ta yi rashin daraktan agaji na Katsina, Alhaji Abdullahi Bakori, wanda Sheikh Bala Lau, ya bayyana a matsayin mutum mai riƙon amana.
Shugaban malaman Ondo kuma babban limamin Owo, Sheikh (Dr) Imam Alhaji Mayor Ahmad Olagoke Aladesawe ya rasu yana da shekara 91 a duniya a jihar Ondo.
Izala a Kano ta bukaci 'yan sanda, DSS da gwamnatin Kano ta dauki mataki kan zargin 'yan Darika da kona mata masallaci da kai wa limami hari a Mauludin Takutaha
Gwamna Umar Bago ya ce dole malamai da limamai a jihar Neja su mika hudubarsu domin tantancewa kafin su yi, abin da ya haifar da martani daga malamai da CAN.
Rahotannin da muke samu sun ce matashin dan sa-kai ya bude wuta a masallaci a ƙaramar Danko Wasagu da ke jihar Kebbi inda aka samu raunuka game da lamarin.
Fitacciyar jarumar fina-finai a Najeriya kuma furodusa, Debbie Shokoya ta bayyana cewa tun farko tana mutunta kowane addini, ta musulunta bayan aure.
Dr. Maryam Shetty ta kammala gasa ta farko ta karatun Alƙur’ani a Kano, inda Nuraddeen Mu’azu ya zama zakara, kuma ya samu N1m, yayin da aka yi addu’ar zaman lafiya.
Musulmai
Samu kari