Musulmai
Dakarun yan sandan Najeriya sun damke mutane 30 da ake zargi da aikata ayyukan ta'addanci da wasu miyagun laififfuka a wuraren tarukan Maulidi a Minna.
Rikicin addini ya barke a Bangladesh wanda ya yi sanadin mutuwar wani, ‘yan sanda sun fara farautar masu tsattsauran ra’ayi bayan sun tono kabarin malami Nurul Haque
Kungiyar Izala reshen Kankia ya sanar da rufe masallacin Juma'a sakamakon ambaliyar ruwan da ta mamaye shi, ta fara shirye shiryen gina sabon masallaci.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya jagoranci sallar Juma'a a wani masallaci da kwamishinan ilimin jihar Dr. John D.W. Mamman da Kirista ne ya gina.
A labarin nan, za a ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf zai kaddamar da Majalisar Shura da ake sa ran zai taimaka wa gwamnatin wajen gano matsalolin jama'a.
wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wani masallaci a jihar Kwara yayin da ake sallar Isha. Sun kashe wani mutum mai suna Alhaji Dahiru.
A labarin nan, za a ji cewa kungiyar kare hakkin Musulmi ta Najeriya (MURIC) ta bayyana takaicin yadda jama'a suka dura a kan matar da ake zargi da kalaman batanci.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa an sanar da rasuwar babban malamin Musulunci a Kano, Sheikh Manzo Arzai a yau Lahadi 31 ga watan Agustan 2025.
Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da biyan alawus ga limamai da ladanai tare da tallafa wa masallatan Juma’a domin karfafa addini da koyar da Alkur’ani.
Musulmai
Samu kari