Musulmai
Biyo bayan sanar da ranar Lahadi, 7 ga watan Yuli a matsayin ranar 1 ga watan Muharram na shekarar 1446, jihohi irin su Sokoto, Ƙebbi, Osun duk sun bada hutu.
Tarihi ya nuna cewa an fara amfani da kalandar Hijira ta Musulunci ne a zamanin mulkin Umar dan Khaddabi biyo bayan sabani da aka samu a kan rarrabe tsakanin shekaru
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ba da hutu a jihar domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH. Gwamnan ya ce ba aiki a ranar Litinin.
Kakakin Majalisar jihar Lagos, Mudashiru Obasa ya magantu kan yiwuwar samar da dokar hana barace-barace a jihar domin ba gwamnatin ikon daukar matakai.
Gwamnatin jihar Borno ta ayyana ranar Litinin, 8 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar. Gwamnatin ta ba da hutun ne domin shigowar sabuwar shekarar musulunci.
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya shawarci Musulmai kan ba da Zakka ga mabukata da marasa karfi inda ya ce hakan zai rage talauci a tsakanin al'umma.
Kungiyar Muslim Media Practitioners of Nigeria (MMPN) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da sauran jihohi su sanya 1 ga watan Muharram a matsayin ranar hutu.
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar hutu domin shigowa sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH. Gwamnatin ta ce babu aiki a ranar Litinin, 8 ga watan Yulin 2024.
A yau ne babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki ta ci gaba da sauraron shari'ar matashin da ya kashe mutane 23 a karamar hukumar Gezawa a Kano.
Musulmai
Samu kari