Musulmai
Fitaccen malamin Musulunci, Farfesa Mansur Yelwa ya bukaci shugabannin kungiyoyin addini da su kira mabiyansa domin fara 'Alkunut' a masallatai madadin zanga-zanga.
Gwamnatin jihar Katsina ta kafa kwamiti da zai binciki jami'an hukumar Hisbah bisa kisan wani mai sana'ar faci a yayin wani bikin aure bayan sun kai samame.
Hukumar Hisbah reshen jihar Katsina ta bayyana kamawa da lalata kwayoyi da giya da suka kai darajar miliyan sittin a karamar hukumar Funtua dake jihar.
Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Muhammad Adam Albaniy ya yi tsokaci kan shirin raba tirelolin shinkafa inda ya ba shi ne mafita ba.
A yau Asabar 20 ga watan Yulin 2024 aka gayyaci Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero zuwa addu'a ta musamman da aka shirya a gidan Khalifa Isyaka Rabiu a jihar.
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki, ta sanya ranar 1 ga Agusta domin yanke hukunci kan matashin da ake zargin ya kashe masallata a Kano.
A gobe Talata al'ummar Musulmi a fadin duniya za su yi ranar Ashura, ana bukatar Musulmi su yi ibada masu muhimmanci a ranar wanda Legit ta tattaro muku su.
Sheikh Ahmed Gumi ya ce malamai su bar kwatanta Najeriya da Sudan ko Libya saboda ba daya suke ba inda ya ce matasa su yi abin a hankali wurin yin zanga-zanga.
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya caccaki matasa kan zanga-zanga inda ya ce ba su da tarbiyya ganin yadda suke cin mutuncin malamai.
Musulmai
Samu kari