Musulmai
Sheikh Murtala Bello Asada ya nuna takaici yadda wasu shugabanni suke tsoron Trump fiye da Allah, yana cewa hakan alamar azzalumai ne masu son duniya.
Majalisar Shari’a ta ƙasa ta bukaci Bola Tinubu ya sake nazarin nadin Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban INEC kan zargin rubuta takarda da ta soki Musulmai.
Kungiyar MURIC ta soki Amurka kan kira da ta yi na a soke Shari’a da barazanar kakabawa gwamnonin Arewa 12 takunkumi, tana kiran hakan matsayinta rashin adalci.
Fusatattun matasa sun kashe limami a jihar Kwara bisa zarginsa da maita; ‘yan sanda sun kama mutane hudu, yayin da aka gargadi jama’a kan ɗaukar doka a hannu.
Wasu kungiyoyin musulami akalla 10 sun garzaya kotu, sun shigar da Gwamna Abba da wasu mutum biyu a gaban kotu kan zargin batancin da ake wa Malam Triumph.
Gwamnatin Jamus ta haramta ƙungiyar Muslim Interaktiv, ta kuma yi samame a gidaje saboda zargin goyon bayan kafa tsarin Musulunci da ayyukan da suka sabawa doka.
Malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce watarana Musulmi zai shugabanci Amurka. Ya yi magana ne bayan nasarar Zohran Mamdani a New York.
Fitaccen mawakin Najeriya, Burna Boy ya fadi dalilin karbar Musulunci bayan dogon nazari da bincike da ya yi. Burna Boy ya fita daga Kiristanci zuwa Musulunci.
Majalisar Amurka za ta yi bincike kan zargin saka dokokin da suke da alaka da shari'ar Musulunci a Najeriya. Najeriya ta yi watsi da cewa an tauye addini a kasar.
Musulmai
Samu kari