Musulmai
Yayin da ake shirin aikin Hajjin 2026, Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta fitar da ka'idoji da suka shafi tashi zuwa Saudiyya da lafiyar mahajjata.
Kungiyar Mangu Concerned Muslim Consultative Forum (MCMCF) ta karyata ikirarin Fasto Ezekiel Dachomo cewa an mayar da cocinsa da aka ƙone a Mangu zuwa masallaci.
Kungiyar MURIC ta nesanta kanta daga kiran wani masanin Amurka da ya bukaci gwamnatin Tinubu ta soke Shari’a da Hisbah, tana kiran hakan kutse cikin ikon Najeriya.
Majalisar Dokoki ta Amurka ta nemi a matsa wa gwamnati lamba ta soke dokar Shari’a da kawar da Hisbah, suna zargin suna tayar da barazanar addini.
Rahoton cibiyar IIFL ta fitar ya nuna cewa kashe kashen da ake a duniya a kan Musulmai musamman hare haren Isra'ila a Gaza ya sanya 'yan Birtaniya shiga Musulunci.
Falasdiawa 54 sun angwance a Gaza bayan shafe shekaru Isra'ila na kai musu hari. Amare da angwaye a Gaza sun nuna farin ciki tare da fatan samun zaman lafiya.
Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wa iyalansa da sauran al'ummar musulmi wasiyoyyida dama musamman a cikin karatuttukansa, an zakulo guda tara daga ciki.
Kungiyar Kwara Inclusion Advocates (KIA) ta sake kiran a samu gwamna Kirista a Kwara a 2027, tana cewa tsarin mulki ya daɗe yana fifita bangare ɗaya.
Rahoton kungiyar mazauna Jos ta JCDA ya ce an kashe Musulmai akalla 4,700 a rikice rikicen da aka yi a jihar Filato a tsawon shekaru. An yi taron addu'a a jihar.
Musulmai
Samu kari