Musulmai
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa an samu ƙarin adadin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa sakamakon harin masallaci a yankin Gezawa ranar Laraba.
Ministar harakokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta janye karar da ts shigar kan kakakin Majalisar jihar Niger kan shirin aurar da mata marayu 100 a jihar.
Kungiya mai kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi martani ga ministar harkokin mata kan hana auren marayu 100 a jihaar Neja. Shugaban kungiyar na Kano ne ya yi martanin.
Gwamna Nasir Idris na jihar Ƙebbi ya shaida tashin tawagar alhazan farko da suka bar Najeriya zuwa Madinah a ƙasar Saudiyya domin gudanar da hajjin bana 2024.
Rundunar ƴan sandan Kano ta bayyana cewa a yanzun mutum takwas ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da aka kai masallaci a ƙaramar hukumar Gezawa.
Rundunar ƴan sandan Kano ta bayyana cewa Shafi'u Abubakar ya aikata laifin da ake zarginsa na ƙona masallaci ne saboda nuna fushin kan rabon gadon gidansu.
'Yan sanda sun tabbatar da cewa matashin da ya babbaka masallata a kauyen Gezawa ya yi amfani da bam wajen aikata ta'adin. Amma an gano ba harin ta'addanci ba ne.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya roƙi ɗaukacin al'ummar Musulmi su fita su fara duba jinjirin watan Zhul Qa'ada yau Laraba.
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta saki sakamakon dalibai dari biyar da talatin da daya da ta rike bisa zargin aikata laifuka daban daban.
Musulmai
Samu kari