Masu Garkuwa Da Mutane
Wasu tsagerun yan bindiga sun tare motar kamfanin sufurin Edo-Line wanda na gwamnatin jihar Edo ne, sun yi awon gaba da fasinjoji 18 ranar Juma'a.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da sace basaraken gargajiya na Bagaji Odo, David Wada, yayin da yake dawowa daga wani taron sarakuna.
Rundunar 'yan sanda ta kama wasu masu garkuwa da mutane a jihar Kano. An kama su bayan wanda suka sace ya gane daya daga cikin masu garkuwa da mutanen.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama masu garkuwa da mutane tare da bindiga 8 da sauran kayan maye da yan daba a watan Agustan shekarar 2025 da ya wuce.
An kama shugaban ’yan bindiga Yusuf Muhamed a Orokam, Benue, bayan ya addabi al’umma; yanzu yana hannun ’yan sanda tare da wasu mutum 21 ana bincike.
Dakarun yan sanda sun mamaye dazuka bayan samun labarin yan bindiga sun sace Fasto Akesinro, ma'aikaci a asibitin FMC na gwamnatin tarayya da ke Ondo.
A labarin, nan, za a ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta bayyana cafke mata da miji da su ka shirga karya cewa an yi garkuwa da data daga cikinsu.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kebbi sun samu nasarar hallaka wasu masu garkuwa da mutane. 'Yan sandan sun kashe su ne bayan an gwabza artabu.
‘Yan bindiga sun kakaba harajin N15m kan garuruwan Katsina, inda suka ce biyan kudin ne kawai zai sanya su daina kashe mutane da yin garkuwa da su a yankin Almu.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari