Masu Garkuwa Da Mutane
Sanata Ali Ndume ya bukaci karin kokari daga gwamnati kan tsaro bayan sace dalibai da ke zana jarabawar NECO a Borno, inda sojoji suka fara aikin ceto.
An yanke wa wasu mutum biyu, Ibrahim Abubakar da Abdullahi Abubakar, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kotu ta same su da laifin garkuwa da mutane.
Dakarun sojoji karkashin Operation ENDURING PEACE sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su daga dajin Pandam a jihar Filato bayan wani samamen dare.
'Yan bindiga sun sace iyalan shugaban APC na karamar hukumar Yauri a jihar Kebbi, Alhaji Yusuf Alhassan. An sace matar shi da dan shugaban APC a Kebbi.
Gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo ya yi barazanar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane da ‘yan daba da aka kama a jihar inda ya ce za a rataye su.
Dakarun rundunar tsaro ta jihar Edo sun cafke wani babban dan garkuwa da mutane da ya addabi al'umma a yankin Uromi da kewaye, sun fushe gidansa.
Rundunar 'yan sandan Najeriya da ke jihar Edo ta yi nasarar kashe wani da ake zargi da garkuwa da mutane. Za a kafa kotu domin hukunta 'yan ta'adda.
Babbar kotun jihar Kogi ta sami wani jagoran dabar yan bindiga, Jibrin Halilu da laifin garkuwa da makwabcinsa tare da kashe shi, ta umarci a rataye shi.
Wasu da ake zargi ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da sace 17 a hare-haren Sabon Birni da Wurno a jihar Sokoto, ciki har da mata da yara marayu.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari