Masu Garkuwa Da Mutane
Yayin da ake rade-radin rasuwar mahaifiyar mawaki Rarara, jaruma Aisha Humairah ta karyata labarin inda ta roki mutane da su bar yada jita-jita babu dalili.
Shugaban kungiyar Patriot for the Advancement of Peace and Social Development (PAPSD), Dakta Sani Shinkafi, ya fadi hanyar shawo kan rashin tsaro a Arewa maso Yamma.
'Yan bindiga da suka sake alƙali Janet Gimba ta kotun gargajiya a Kaduna sun sake ta. Sun buƙaci kudin fansa N150 miliyan nan da kwana 6 ko su cutar da 'ya'yanta.
Rundunar ta yi holin matasa akalla 149 da aka kamo daga cikin loko da dakunan Kano a tsakanin kwanaki 10 da fara aikin sabon kwamishinan yan sanda.
Miyagun 'yan bindigan da suka yi garkuwa da wata alkaliya tare da 'ya'yanta a jihar Kaduna sun bukaci a ba su makudan kudade a matsayin kudin fansa.
Gwamnan jihar Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia ya sanar da sa dokar zaman gida a ƙaramar hukumar Ukum da kewaye biyo bayan ɓarkewar zanga-zanga a yankin.
A safiyar yau ne 'yan ta'adda su ka kai hari garin Ayati a karamar hukumar Ukum inda su ka kashe mutane 11 ba haira ba dalili, wannan ja jawo mutane yin zanga-zanga.
Babbar kotun jihar Osun ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga masu garkuwa da mutane da suka kashe wani Bafulatani bayan sun yi garkuwa da shi.
'Yan bindigan da suka sace mahaifiyar Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara sun bukaci a ba su N900m a matsayin kudin fansa kafin su sako ta.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari