Masu Garkuwa Da Mutane
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne. Jami'an tsaron sun kuma kwato makamai a hannunsu.
'Yan banga da mafarauta sun kashe ‘yan bindiga yayin wani artabu a dajin Achido, sun kuma ceto mutane 14, ciki har da Abdullahi da aka sace makonnin baya.
Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace mutane sama da 100 a Zamfara. Cikin waɗanda aka sace akwai mata, yara ƙanana da limamin garin aka tafi da su.
Yan sanda sun yi gumurzu wajen ceto matafiya 19 da aka sace a jihar Neja. Matafiyan sun fito ne daga jihar Sokoto zuwa Bayelsa kuma an mayar da su gida.
Rundunar 'yan jihar Bauchi ta samu nasarar hallaka wasu masu garkuwa da mutane bayan sun yi wata arangama. 'Yan sandan sun kuma kwato makamai masu yawa.
Kakakin majalisar dokokin jihar Neja ya tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace mutane 22 da suka tare motoci biyar a titin zuwa Kontagora ranar Alhamis.
Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani dan kasuwa a jihar Ebonyi. Yan bindigar sun harbe dan kasuwar tare da ƙona gawarsa a cikin gidansa.
Maharan da suka yi garkuwa da limamin coci a jihar Edo sun tuntuɓi ƴan uwansa sun bukaci lale masu kudi fansa Naira Miliyan 200 kafin da su sake shi.
Wani limamin cocin katolika, Rabaran Tsomas ya nuna halin dattako, inda ya mika kansa ga ƴan bindiga domin su saki ɗalibai 2 da suka yi garkuwa da su a Edo.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari