
Manyan Labarai A Yau







Mai magana da yawun shugaban hukumar zaɓe watau INEC ya buƙaci ƴan Najeriya su yi watsi da jita-jitar da ke nuna cewa shugaba Tinubu ya tsige Mahmud Yakubu.

CRACON ta roki Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin bincike kan Ministan Tsaro, Badaru, bisa zargin cin hanci da sabawa doka ta hanyar gudanar da kasuwanci na sirri.

'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina. 'Yan bindigan sun hallaka mutane tare da raunata wasu daban.

Jami’an ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da fatattakar masu zanga-zanga a Fatakwal, jihar Rivers inda suka kuma doki wasu ciki har da ‘yan jarida.

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana jam'iyyar APC ta lallaba shi domin ya yi takarar sanatan Edo ta Tsakiya a babban zaben shekarar 2023.

Na kusa da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Petwr Obi, ya yi magana kan shirinsa na ficewa zuwa jam'iyyar adawa ta SDP.

Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin kwanton bauna ga sakataren gwamnatin jihar Plateau. 'Yan ta'addan sun kai farmakin ne a karamar hukumar Bokkos.

Dakarun sojojin Najeriya sun yi artabu mai tsanani da 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno. An samu asarar rayuka a bangarorin sojoji da na 'yan Boko Haram.

Gwamnatin jihar Yobe ta fito ta yi magana kan wasu rahotanni da aka yada A shadangane da batun 'yan ta'addan Boko Haram sun tunkaro birnin Damaturu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari