Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya ce Donald Trump na da ikon mulkin Amurka kawai, ba shi da damar tilasta wa sauran ƙasashe bin dokokinsa.
Hakimin Gwandu, Alhaji Muhammadu Rasheed, ya rasu a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, inda za a yi sallar jana’izarsa a fadar Sarkin Gwandu da ke Birnin Kebbi.
Mutane huɗu, maza biyu da mata biyu, sun mutu bayan wani ramin hakar ma’adanai ya ruguje a yankin Baban Rafi da ke karamar hukumar Bokkos, Plateau.
Karamin Ministan Man Fetur Heineken Lokpobiri ya ce matsakaicin farashin fetur a Najeriya har yanzu ya fi na Amurka da wasu ƙasashen Afirka sauƙi.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Iuwa Yahaya, ya amince da naɗin sababbin kwamishinoni uku, masu ba shi shawara biyu da manyan mataimaka huɗu a gwamndti.
An kashe mataimakin kwamandan Operation Rainbow, CSP Dennis David Babale, bayan ’yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro kwanton bauna a jihar Plateau.
Aliko Dangote ya ce gidauniyarsa za ta haɗa gwiwa da gwamnatocin jihohi domin taimaka wa mata masu rauni miliyan biyu su mallaki hannun jari a matatar Dangote.
Omoyele Sowore ya nemi Majalisar Tarayya ta yi amfani da Sashe na 145(2) na Kundin Tsarin Mulki domin bai wa Kashim Shettima damar riƙon Shugaban Ƙasa.
Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnatin NDC ƙarƙashin Peter Obi za ta dawo da tallafin man fetur ta wata hanya, ta hanyar ƙara samar da fetur a cikin gida
Manyan Labarai A Yau
Samu kari