Manyan Labarai A Yau
Jigo a jam'iyyar APC, Denge Onoh ya roƙi Shugaba Tinubu ya sa baki kan shari’ar Nasir El-Rufai tare da yin la’akari da yi masa afuwa domin ƙarfafa sulhu.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya naɗa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na jam’iyyar ADC.
Gwamnatin Tarayya ta ce inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro ya taimaka wajen kama ɗan ta’adda Mamuda da babban mataimakinsa ba tare da an yi harbi ba.
Fadar Gwamnatin Benue ta mayar wa madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso martani kan kalamansa game da rikicin Hyacinth Alia da George Akume.
Kenneth Okonkwo ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na guje wa zuwa kasar Amurka ne saboda tsoron yiwuwar Shugaba Donald Trump ya sa a kama shi.
Atiku Abubakar ya ziyarci Minna jihar Neja inda ya jajanta wa iyalan masu haƙar ma’adanai 37 da suka mutu a hannun NSCDC, tare da ba da tallafin N20m.
’Yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ISWAP sun kai hari Wumbi a Borno, inda suka kashe kwamandan ’yan banga da fararen hula huɗu tare da jikkata wasu.
A taron New Yorkz Gwamnatin Tarayya da ƙasar Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin bunƙasa fannin ma’adinan ƙasa na Najeriya.
Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta umarci PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar bayan kalubalantar tikitin Farfesa Isa Pantami.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari