Manyan Labarai A Yau
Firaministan kasar Israila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa ana muzgunawa Kiristoci a Najeriya. Ya nuna cewa yana aiki don kawo musu dauki na musamman.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana halaye 6 da ke kai mutum Aljanna, tare da ba da shawara kan kiyaye fushi a wata nasiha da ya turo daga birnin Landan.
EFCC ta gurfanar da kwamishinan Bauchi kan zargin tallafa wa ta’addanci da dalar Amurka $9.7m; an tura shi gidan yarin Kuje yayin da yake jiran hukuncin beli.
Sabuwar hukumar tattara haraji ta Najeriya watau NRS ta fara aiki bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu, an fitar da tambarin hukumar.
Wata babbar kotu ta Abuja ta ba gwamnatin tarayya damar fara aiwatar da sababbin dokokin haraji. Ta ki amincewa da bukatar da aka shigar a gabanta.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi wa Peter Obi maraba zuwa jam'iyyar ADC. Ya ce shigowarsa na da muhimmanci ga adawa a Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC. Peter Obi ya ce suna da shirin ceto Najeriya.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta tanka bayan Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba ta da matsguni a siyasar jihar Rivers.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Nasarawa. 'Yan bindigan sun kashe mutane tare da raunata wasu daban bayan sun farmake su.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari