Malaman Makaranta
A labarin nan, za a ji cewa kungiyoyin SSANNU da NASU sun kara bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin tafiya yajin aiki a kan bukatunsu, an kara makonni biyu.
Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti ya amince da rancen Naira miliyan 596.6 ga malamai da ma’aikatan makarantun sakandare don su sayi motoci da gidaje.
Gwamnatin jihar Gombe ta ja kunnen iyayen yara kan batun sanya yara a cikin makaranta. Ta bayyana cewa iyayen da ba sa kai yara makaranta za su fuskanci dauri.
Dalibai bakwai sun jikkata a Ukum, Benue bayan wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya tashi a makarantarsu. ‘Yan sanda da gwamnati sun dauki matakai kan lamarin.
Gwamna Bala Mohammed ya amince da korar wani babban jami'i a ma'aikatar ilimi ta Bauchi, Emos Joshua bisa zargin cin zarafin dalibai a kwalejin gwamnati, Azare.
ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki a fadin Najeriya kan gazawar gwamnati na cika alakawuran da ta dauka a 2009, yayin da minista ya musanta wanzuwar yarjejeniyar.
Gwamna Namadi ya ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi a Jigawa bayan da aka gano yara 8 cikin 10 ba su iya karatu ko rubutu ba. Ya dauki malamai 10,000 aiiki.
Ana kashe biliyan 2.354 duk wata kan sanatoci 109, wanda ya isa biyan albashin farfesoshi 4,708, yayin da farfesa ke samun kusan 500,000 kacal a wata.
Gwamnatin Najeriya za ta fara ba iyaye tallafin kudi domin mayar da yara makaranta. An bayyana shirin karin kudin tallafin karatu ga dalibai a matakai daban daban
Malaman Makaranta
Samu kari