Malaman Makaranta
Gwamnatin Gombe ta umarci makarantun jihar su kulle zuwa ranar Juma'a. An umarce su da su yi jarrabawa cikin gaggawa domin sallamar dalibai saboda barazanar tsaro
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin Bauchi ta ce a rufe makarantun firamare, sakandare da na gaba da sakandare mallakkinta da masu zaman kansu saboda sace dalibai.
Gwamnatin tarayya karkashin jagoranci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta karyata labarin da ke yawo cewa ta ba da umarni rufe duk wata makarantar gwamnati.
Filato da Katsina sun rufe dukkan makarantu saboda barazanar tsaro da hare-haren garkuwa da dalibai. Gwamnatoci na cewa matakin na wucin gadi ne domin kare rayuka.
Gwamnatin tarayya ta ba da shugabannin makarantu 47 umarnin kullewa nan take yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a wasu sassan kasar nan.
Wani ganau ya bayyana cewa wasu daga cikin daliban da yan bindiga suka kwasa daga makarantar Katolika da tsakar dare sun tsere bayan mota ta lalace.
Gwamnatin Katsina karkashin Gwamna Dikko Radda ta rufe makarantun firamare da sakandire a fadin jihar saboda dalilai na tsaro bayan farmakin da aka lai Neja.
Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya yi magana kan sace dalibai da aka yi a jihar Neja. Gwamna Umaru Bago ya ce tun a karon farko an nemi a rufe makarantar.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da daukar malaman lissafi 400 domin cike gibin karancinsu a makarantun sakandire na gwamnati da inganta ilimi.
Malaman Makaranta
Samu kari