Lucky Aiyedatiwa
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya kare gida, ya samu nasarar doke abokan hamayya a rumfar zaben da ya kaɗa kuri'a a zaben gwamnan da aka yi a jihar Ondo yau Asabar.
Sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo na ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024 ya fara fitowa daga rumfunan zabe, gundumomi da kananan hukumomin jihar.
Dan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ondo, Olayide Adelami, ya lashe zabe a rumfar zabensa. APC ta lallasa PDP a rumfar zaben.
Wani jagoran APC a jihar Ondo ya ce za su samu nasara a zaben gwamna da ake gabatarwa a jihar. Dan APC ya ce babu wata jam'iyyar adawa da za ta iya ja da APC.
Dan takarar jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP), Dr. Abass Mimiko, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai tsoma baki ba a zaben gwamnan Ondo.
Jam'iyyar APC ta kakryata zargin PDP na cewa ta tura 'yan daba zuwa karamar hukumar Idanre domin hargitsa zaben gwamnan jihar Ondo. APC ta ce zancen kawai ne.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ke takarar gwamnan Ondo a jam'iyyar APC a zaben da ake yi ya ce zai karbi kaddara idan aka yi adalci ko da bai yi nasara ba.
Jam'iyyun siyasa sun ci kasuwar sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Ondo da ake yi yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024, an rika ba mutane takarda.
Rahotannin sun tabbatar da cewa yan daba sun yi ta harbe-harbe wanda ya tilasta mazauna wan yankin Ondo shigewa gidajensu saboda fargaba ana tsaka da zabe.
Lucky Aiyedatiwa
Samu kari