Kananan hukumomin Najeriya
Majiyoyi sun tabbatar da cewa masu zanga-zanga sun bankawa ofishin hukumar zabe ta INEC wuta a Niger yayin da ake jiran sakamakon zaben kananan hukumomi.
Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya rattaba hannu kan dojar kafa sababbin kananan hukumomi 29, an tura sunayensu ga Majalisar Tarayya don amincewa.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya ayyana ranakun Alhamis da Juma'a, 30 da 31 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin hutu saboda zaben kananan hukumomi.
Babbar kotun tarayya ta Abakaliki ta soke zaben kananan hukumomi a Ebonyi, ta tsige shugabanni 13 da kansiloli 171, ta ce an karya dokar zabe ta kasa.
Wasu fusatattun matasa sun farmaki shugaban karamar hukumar Egor, Hon. Osaro Eribo yayin tabbatar da bin ka'ida kan cunkoso a jihar Edo a yau Lahadi.
An yi rashi a jihar Bauchi bayan rasuwar daya daga cikin shugabannin kananan hukumomi. Gwamna Bala Mohammed ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin.
Wasu mata hudu 'yan siyasa, da aka zabe su a mukamai daban daban a Legas sun rasu cikin kwanaki 57 kacal bayan rantsar da su, APC ta karyata zargin siyasa a ciki.
Wata biyu kacal da rantsar da ita kan karagar mulki, mataimakiyar Shugaban Karamar Hukumar Badagry ta Yamma a jihar Legas, Princess Oluremi Ajose, ta rasu.
A labarin nan, za a j icewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da tabbacin dawowar zaman lafiya Ribas bayan watanni shida da dokar ta baci a jihar.
Kananan hukumomin Najeriya
Samu kari