Matawalle
Karamin Ministan Tsaro a Najeriya, Dr. Bello Matawalle, ya musanta zargin alaka da yan ta’adda, yana kalubalantar masu zargi su kai shi kotu da hujjoji.
Dan bindiga, Bello Turji ya fito da sabon bidiyo yana karyata zargin cewa Bello Matawalle ya ba ’yan bindiga kuɗaɗe, yana cewa ba a taba ba shi miliyoyi ba.
Malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya ce karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya taka rawar gani wajen samar da tsaro a jihar Zamfara.
Wani wanda ya bayyana kansa a matsayin tsohon hadimin karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce ya shirya ba da shaida a gaban kotu a kansa.
Ministan Tsaro Bello Matawalle ya kai ƙara kotu domin dakatar da kafofin yaɗa labarai daga wallafa rahotannin da ke zarginsa da alaƙa da ’yan ta’adda.
Tsohon sanatan Zamfara ta Arewa, Kabiru Marafa, ya ragargaji karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle. Ya bayyana irin taimakon da ya yi masa wajen zama gwamna.
Kasar Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro na shekaru biyar domin karfafa hadin gwiwa ta horo, leken asiri, kera makamai a tsakaninsu.
Bello Matawalle ya ce masu sukarsa na yada karya ne saboda siyasa, ya bayyana cewa ya gaji matsalar tsaro tun kafin gwamnatinsa ta ɗauki matakan magance ta.
Wasu masu amfani da intanet sun sake magana kan tsohon bidiyon Bello Matawalle na 2021, inda yake kare wasu ’yan bindiga da ake ganin bai kamata ba.
Matawalle
Samu kari