Jihar Legas
Tsohon Antoni-Janar na jihar Legas, Farfesa Alfred Kasunmu, ya rasu a ranar Lahadi, bayan ya shafe shekaru yana koyarwa da kuma gudanar da aikin lauya.
Hukumar kwastom ta kama wasu bindigogi kusan 400 da aka yi yunkurin shigowa da su Najeriya yayin da ake kokarin shirye shiryen zaben 2027 a fadin kasar nan.
Wanda jarumar Nollywood Temitope Osoba za ta aura ya yi zargin cewa ta rasu a ofishin ’yan sanda a, Legas, yana mai musanta cewa ciwon kansar nono ne ya kashe ta.
Mijin tsohuwar Ministar Kuɗi, Kemi Adeosun, Anthony Adeosun, ya rasu yana da shekara 62 a duniya, kamar yadda iyalansa suka sanar a cikin wata sanarwa.
Matatar Dangote da ke jihar Legas ta rage farashin fetur zuwa N1,165 kan kowace lita daga N1,215, sannan ta sauke farashin dizal zuwa N1,570 a Najeriya.
Hukumar FAAN ta tabbatar da tashin gobara a wani bangare na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas. Rahotanni sun ce ba a samu asarar rai ba.
Alkalin Alkalai a Najeriya ta haramta amfani da lakabin “Barrister” a mu’amalar hukuma da Kotun Koli, tana mai cewa bai dace da ƙa’idojin ƙwarewar aiki ba.
Mutuwar Emmanuel Abiodun Adewale Alogbo, shugaban cocin Cherubim and Seraphim Movement na duniya baki ɗaya, ta jawo saƙonnin ta'aziyya daga al'ummar Kiristoci.
Sheikh Surajudeen Akanni, wanda aka fi sani da Arizukuna, ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, yayin da malamai da iyalansa suka bayyana alhininsu.
Jihar Legas
Samu kari