
Jihar Legas







'Yan ta’adda sun farmaki ofishin jam'iyyar LP a Legas, inda suka sace muhimman kayayyaki da makudan kudade. LP dai ta zargi Gwamna Otti da cin amanar jam’iyya.

Masu zanga-zanga sun mamaye manya tituna a Abuja, Legas da Fatakwal don su nuna adawa da mulkin Tinubu, duk da gargaɗin da ‘yan sanda suka bayar.

Farashin abinci kamar shinkafa, doya, wake da gyada na ci gaba da sauka a Najeriya, wanda ya faranta ran magidanta da iyalai a jihohin da abin ya fi shafa.

Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta kama wani mahaifi da zargin kashe 'yarsa mai suna Shakirat Ojo ya birne ta. An tono gawar bayan kwanaki takwas domin bincike.

Gwamna Babajide Sanwo Olu na jihar Legas ya nemi afuwar ƴan Najeriya kan cunkoson da ya faru sakamakon fara aikin gadar Independence, ya ce aikin zai shafe makonni.

Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya kara kudin litar man fetur a Najeriya 'yan sa'o'i da sauke Mele Kyari da Bola Tinubu ya yi. Ana sayar da litar mai a N950.

Hadakar jam'iyyun PDP ta yi tir da wasu rahotanni da ke bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar ya nemi gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu don neman takararsa.

Atiku ya musanta karbar kudi daga Sanwo-Olu, yana mai cewa zargin karya ne. Tawagarsa ta bukaci EFCC ta bayyana bincikenta, domin dakile makircin 'yan siyasa.

Majalisar wakilai a yau Laraba 26 ga watan Maris, 2025 ta amince da kudirin dokar da zai mayar da kananan hukumomi a jihar Lagos guda 57 daga 20.
Jihar Legas
Samu kari