Labarin Sojojin Najeriya
Wata mummunar arangama tsakanin jami’an sojin ruwa da na ‘yan sanda yayi ajalin ‘dan sanda mai mukamin ASP. An gano cewa har da masu wucewa 3 lamarin ya ritsa.
Daya daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram da suka mika wuya, Malam Rugurugu ya ce ya hakura ya fito daga jeji ne saboda rokon su da Gwamna Zulum ya yi.
Sojin Najeriya sun yi Lugude kan mayakan ISWAP bayan harin da suka kai kansu a garin Damboa a jihar Borno. Sun isa wurin a motocin yaki da Hilux da makamai.
Mun kawo hukunci masu ban mamaki da aka zartar a kotu, tun daga hukuncin daurin watanni uku a gidan yari ga IGP Usman Alkali Baba zuwa ga na Shugaban EFCC.
Dazu muka samu labari cewa bayan daure Shugaban EFCC da Sufetan 'Yan Sanda, Kotu tace a cafko Shugaban Hafsun Soji da Wani Babban Jami’i, a garkame a gidan yari
Dakarun sojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan ‘yan ta’addan ISWAP Ana tsaka da koya musu amfani da makamai tare da hada bama-bamai a yankin tafkin Chadi.
Jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya yi ruwan bama-bamai har guda bakwai a kan ayarin mayakan kungiyar ISWAP a Damboa ta jihar Borno. Mayaka da dama sun mutu.
Jami'an rundunar sojojin Najeriya sun farmaki mabuyar yan bindiga a garin Tsohon Gayan a yankin Chikun na jihar Kaduna, inda suka aika mayaka hudu barzahu.
Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta fitar da sunayen kwamandojin yan ta'adda 19 da ake nema ruwa a jallo. Yan ta'addan sun dade suna adabar garuruwa da dama a arewa.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari