Labarin Sojojin Najeriya
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaron da ake fuskanta na dab da zuwa karshe. Ya bukaci a ci gaba da addua.
Majiyoyin soji sun tabbatar da cewa hare-haren Amurka a Arewa maso Yamma sun yi nasara, bayan haɗin gwiwa da sojojin Najeriya wajen kai farmaki kan ’yan ta’adda.
Sojojin Najeriya sun cafke fitaccen jagoran ‘yan bindiga Fidelis Gayama a Benue, wanda ake zargi da garkuwa da mutane da fashi a yankin Benue zuwa Taraba.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta biya diyya ga iyalan fararen hula 13 da suka mutu sakamakon harin sama da aka kai bisa kuskure a jihar Sokoto.
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta tsare tsohon ministan tsaro, Candide Azannai, bisa zargin hannu a yunkurin juyin mulki da aka dakile a farkon Disambar 2025.
Bayan sakin sojojin Najeriya, ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya isar da sakon zumunci daga Bola Tinubu zuwa Shugaban Burkina Faso, Ibrahim Traoré.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya ziyarci Ibrahim Traore na kasar Burkina Faso. An saki sojojin saman Najeriya 11 da aka rike a kasar da jirginsu.
A labarin nan, za a ji cewa wasu manyan sojoji a Najeriya sun sa baki a kan yunkurin da aka dauko na kara wa dogarin Shugaban Kasa Bola Tinubu girma.
Harin jiragen saman NAF a Kukawa, jihar Borno, ya hallaka fararen hula ciki har da masunta da direbobi, yayin da ake binciken sahihancin bayanan sirri.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari