Labarin Sojojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya da ke karamar hukumar Mangu a jihar Plateau ta hallaka tsagera 'yan bindiga uku da kwato muggan makamai a hannunsu bayan wani artabu.
Majalsar dattawan Najeriya ta amince da naɗin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa sabbin hafsoshin tsaron ƙasa. Majalisar ta amince da naɗin ne bayan tantancesu.
Majalisar dattawa ta fara tantance manyan hafsoshin ƙasar nan da shugaba ola Tinuu ya naɗa. Majalisar dattawan za ta tantance su ne bayan Tinubu ya bukaci haka.
Dakarun sojoji na atisayen 'Operation Safe Haven' sun yi arangama da miyagun ƴan bindiga a jihar Plateau. Sojojin sun halaka ƴan bindiga uku da kwato makamai.
Rundunar sojin Najeriya ta cafke wani sojan bogi a Port Harcourt cikin jihar Rivers da ke ikirarin shi Kofur ne na soja tare da karbar kudade a hannun mutane.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasarar ceto mutum 30 da ƴan ta'adda suka sace a jihar Kebbi. Jami'an tsaron sun ceto mutanen ne a cikin kwana biyu.
Dazu aka ji NDLEA ta yi nasarar kamo wasu gungun mutanen da ke da hannu a fataucin kwayoyi. A wadanda ake zargi su na fataucin kwayoyi har da ma'aikatan coci
Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun murkushe mayakan ISWAP da dama a wani mummunan hari da suka kai masu ta sama a ranar Laraba, 5 ga watan Yulin nan.
Ganin halin da ake ciki na nadin sababbin hafsoshin tsaro, tsofaffin sojoji da 'yan sanda sun fadi yadda za a inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari