Labarin Sojojin Najeriya
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yi wa 'yan ta'adda raga-raga a sassa daban-daban. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda da dama tare da kwato makamai.
Jami'a tsaro sun kama mutane 22 da ake zargi da shiga kungiyar asiri a jihar Ogun. Cikin mutanen da 'yan sanda suka kama akwai sojoji biyu da wasu mata.
Rundunar sojin Najeriya ta hallaka wani dan bindiga Dan Dari Biyar da ya shahara da kashe mutane da garkuwa da mutane da gallazawa Hausawa a Sokoto.
A labarin nan, za a ji yadda dakarun sojin sama da kasa suka hada kai da mafarauta inda aka fatattaki wasu 'yan ta'adda har maboyarsu da ke Borno da Adamawa.
Jami'an tsaro sun samu nasarar kashe wasu 'yan bindiga yayin wani artabu da suka yi a jihar Zamfara. Jami'an tsaron dai sun shirya musu kwanton bauna ne.
Sojojin Operation Hadin Kai sun fatattaki Boko Haram a Borno, sun kashe kwamandansu Ibn Khalid, sun kwato makamai da bama-bamai, kuma sun hana harin Bitta.
Sojojin Operation Fansan Yamma sun kashe 'yan ta’adda da dama a Rijau, sun kwato bindigogi da babura 18, sai dai soja guda ya rasa ransa yayin fafatawa da maharan.
A labarin nan, za a ji cewa sojojin 'kasar nan sun yi nasarar fatattakar wasu 'yan ta'adda sama da 95 yayin suka baro Zamfara a babura zuwa Neja.
A labarin nan, za a ji yadda rundunar tsaron Najeriya ta yi martani ga Turkiyya bayan ta ankarar da ita kan sabuwar yan ta'adda mai basaja da bayar da tallafi.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari