Labarin Sojojin Najeriya
Rahotanni daga jihar Borno sun tabbatar da tashin wani bam da yara yan gwangwan suka dauko a bayan gari, mutum biyu sun jikkata yayin wasu 4 suka raunata.
Sojin saman Najeriya sun kai farmaki a sansanin 'yan bindiga da ke Danmusa, jihar Katsina, sun kubutar da mutum 62, gwamna Radda ya yaba da jarumtar jami’an tsaro.
Yaran dan ta'adda, Bello Turji sun kai hare hare jihar Sokoto. Sun kashe mutane da dama tare da sace wasu. Sojoji sujn ce har yanzu suna neman Turji ido rufe.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya sanar da cewa jami'an tsaro sun samu nasarar cafke shugaban kungiyar 'yan ta'addan, Ansaru.
Rahotanni daga rundunar sojin Najeriya sun nuna cewa an samu wata fashewa a dakin ajiya da je Barikin Ilese a jihar Ogun amma babu wanda ya rasa ransa.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi magana kan rahotannin da ke cewa tantirin dan bindiga, Bello Turji, ya mika wuya. DHQ ta ce ana ci gaba da farautarsa.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun shirya harin kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihar Zamfara. Harin ya jawo an hallaka masu samar da tsaro da fararen hula.
Boko Haram ta kai kazamin hari Borno, inda ta kashe sojoji, sace ɗaliba, ƙone gidaje, shaguna da motoci wanda ya tilasta mazauna Kirawa tsere wa zuwa Kamaru.
Wasu 'yan ta'adda na kungiyar ta'addanci ta ISWAP sun yi aika-aika bayan sun wani hari a Borno. Magakan kungiyar sun hallaka wani shugaban kungiyar mafarauta.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari