Labarin Sojojin Najeriya
Matasa a Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen fitowa domin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan. Zanga-zangar za a yi ta ne saboda tsadar rayuwa da talauci.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun kafa shingen binciken ababen hawa a titin Keffi-Abuja sa'o'i 24 gabannin fara zanga-zangar tsadar rayuwa.
Rundunar 'yan sandan Kano ta ce an yi zaman taro na musamman a kan shirin gudanar da zanga zanga, inda aka gana da dukkanin shugabannin tsaro a jihar.
Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta cafke Aminu Muhammad da ya shafe shekaru biyu yana damafara da sunan shi soja ne. Ya cuci mutane makudan kudi a jihar.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da nasara da ta samu kan yan ta'adda a jihar Kaduna. Sojoji sun fafata da yan bindigar inda suka kashe biyu suka kwato makamai.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ta gano wasu bata gari da ke shirin sajewa da masu zanga zanga su farmaki mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cato dayadaga cikin matan Chibok da wasu mata da dama bayan sun fafata da Boko Haram an mika mutanen ga gwamnatin Borno.
Hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana hakar ma'adanai da satar shanu cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas wajen yakar yan ta'adda.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an tsinci gawar wani sojan Najeriya da ya yi ritaya a cikin daki a birnin Jos na jihar Plateau. Za a fara bincike kan lamarin.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari