Labarin Sojojin Najeriya
Dakarun sojohin Najeriya sun samu nasara kan miyagun 'yan ta'addan da ke aikata ta'addanci a jihar Kaduna. Sojojin sun kwato makamai masu tarin yawa.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami, ya yi magana kan hanyar kawo karshen 'yan bindiga da sauran matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu yawan gaske a wasu hare-hare a jihohin Kaduna da Zamfara.
A wannan labarin za ku karanta yadda migayu su ka sace Basarake a jihar Kaduna, tare da ɗiyarsa da wasu mazauna yankin Gurzan Kurama da ke jihar Kaduna.
An samu nasarar cafke wani mai garkuwa da mutane a garin Takum na jihar Taraba. An cafke wanda ake zargin ne bayan ya je masallaci domin yin Sallah.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir hakimin Gatawa, Isah Bawa, ya ce ba zai yiwu makasan basaraken su ci bulus ba.
Rahotanni sun ce an kashe ‘yan bindiga da dama da kuma wasu sojoji yayin wani artabu a kauyen Gudiri da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase ta jihar Filato.
Dakarun rundunar sojojin sama sun samu nasarar hallaka manyan kwamandojin 'yan ta'adda a jihar Borno. Sojojin sun kashe su ne a wasu hare-hare ta sama.
Sojojin Najeriya sun samu nasara kan yan Boko Haram bayan sun fafata yayin wani fada da suka yi a Maiduguri. Sojojin sun samu nasarar kashe Abu Rijab da ake nema.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari