Labaran Duniya
Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen attajirin nan ɗan sharholiya, Richard Lugner ya kwanta dama bayan fama da doguwar jinya, ya rasu watanni bayan kara aure.
Matatun man fetur suna da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya. Akwai matatun mai guda 825 da ke aiki. Ga jerin guda 10 da suka fi girma.
Zinariya wata kadara ce mai kima wacce za ta iya inganta ajiyar kudin ketare, rage dogaro ga rancen kasashen waje. Mun tattaro kasashe 10 mafi samar da shi a Afrika.
Rahoton da OPEC ta fitar na watan Yuli ya nuna cewa matatar man Dangote na shirin zama karfen kafa ga masana'antar man Turai yayin da za ta girgiza duniya.
Babban jakadan Biritaniya a Najeriya, Dakta Richard Mongomery, ya tabbatar wa dimbin ‘yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya tabbacin tsaro a lokacin zanga zanga.
Shekaru 15 da Sheikh Hasina ta yi a matsayin Firaministar Bangladesh ya zo karshe a ranar litinin yayin da yi murabus inda kuma sojoji suka karbi mulki.
A cikin watanni 6, Aliko Dangote ya tafka asarar dala biliyan 10, wanda ya sa ya fado zuwa na biyu a jerin masu kudin Afrika yayin da Johann Rupert ya koma na 1.
Firaminstar kasar, Sheikh Hasina ta ajiye aiki sannan ta gudu daga kasar bayan akalla jami'an tsaro sun kashe mutane sama da 300 yayin arangama da jami'an tsaro.
Kungiyar hadin kan kasashen Afrika, ECOWAS ta bukaci kasashen NIjar da Benin su bude iyakokinsu domin saukaka rayuwa da habaka tattalin arzikin al'umma.
Labaran Duniya
Samu kari