Labaran Duniya
Rahoton da Google ya fitar na abubuwan da aka fi bincike a manhajarsa a 2025 ya nuna Sanata Natasha Akpoti ce aka fi karanta labaranta, sai su Muhammadu Buhari.
Daya daga cikin jagororin 'yan adawa a kasar Kamaru, Anicent Ekane ya rasu a hannun sojoji kwanaki bayan Paul Biya ya kama shi saboda wasu zarge-zarge.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya gana da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa kan rikicin siyasar da ta barke bayan juyin mulki a Guinea-Bissau.
Mutanen Utqiagvik a Alaska ba za su sake ganin hasken rana ba tsawon kwanaki 64 bayan fara dogon dare, sakamakon juyawar Duniya da ake samu a shekara.
Hukumar USCIS ta ce ta fara duba yiwuwar kwace damar zama a Amurka ga mutanen ƙasashe “masu matsala”, bisa umarnin Shugaba Donald Trump bayan harbin sojoji.
Gwamnatin Najeriya ta la’anci juyin mulkin soja a Guinea-Bissau, tana cewa matakin ya barazana ga dimokuraɗiyya, tsaro da kwanciyar hankali a yanki baki ɗaya.
Shugaban Amurka Donald J. Trump ya yi magana bayan wani dan bindiga ya harbi sojojin Amurka a kusa da fadar White House. Ya ce barazana ne ga tsaron Amurka.
Rundunar 'yan sandan Washington DC da ke Amurka, ta tabbatar da cewa an harbi sojojin kasa biyu har sun aamu raunuka a kuaa da fadar White House.
Rahotanni daga kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da cewa dakarun sojoji sun kifar da gwamnati, sun sanar da dakatar da shirin zzabe tare da rufe iyakokin kasar.
Labaran Duniya
Samu kari