Kwara
Fitaccen mawaki Senwele, daga jihar Kwara, ya rasu bayan 'yar gajeriyar rashin lafiya. An ce marigayin ya yi fice a salon wakokinsa na Dadakuada mai ban dariya.
Sanatan Kwara ta Tsakiya na jam'iyyar APC, ya yi magana kan jita-jitar cewa ya shirya ficewa daga jam'iyyar. Salihu Mustapha ya ce ko kadan babu batun hakan.
Masarautar Ilorin ta musanta rahoton da aka fara yaɗawa cewa sarki Sulu Gambari da Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara sun fara zaman doya da manja.
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kwara, Alhaji Saka Abimbola Isau, ya yi bankwana da duniya. Marigayin ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 69.
Masu garkuwa da mutane sun sace Farfesa John Ebeh a kofar gidansa, sun kira danginsa suna neman kundin fansar Naira miliyan 10 bayan sun tsoratar da jama'a.
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya fito ya yabi manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya ce manufofin suna yin aiki sosai.
’Yan sandan Kwara tare da hadin guiwar Oke-Ero sun ceto mutane 13 da aka sace, bayan sun yi artabu da maharan. An ce jami'an tsaron sun mayar da mutanen gida.
Prince AbdulƘadir Mahe, shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Kwara ya kwanta dama ranar Asabar da safe, Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya tabbatar.
Tun yanzu wasu sun fara shirye-shiryen zaben 2027 yayin da ake hasashen rigimar siyasa ta kunno kai a jihar Kwara bayan cire allunan tallan Sanata Saliu Mustapha.
Kwara
Samu kari