
Kwara







Bola Ahmed Tinubu ya sauke Mele Kyari a matsayin shugaban NNPCL inda ya maye gurbinsa da Bayo Ojulari da ya fito daga jihar Kwara a Arewa ta Tsakiya.

Gwamnatin jihar Kwara ta nuna alhini kan rasuwar Sheikh Muhammad Jamaalu Deen Yahyah Murtadoh Agodi, wanda ya rasu da safiyar Asabar, 29 ga Maris, 2025.

Mai martaba sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gmabari ya bukaci ƴan siyasa su zama mutane masu faɗin gaskiya komai ɗacinta, sun daina yi wa mutane ƙarya.

Malamin Musulunci a Kwara, Alfa Mohammed Ali Eyonbo Anabi, ya ce mahaifiyar Gwamna AbdulRazaq ta tabbatar musu tun 2019 cewa ɗanta zai yi kokari sosai a mulki.

A wurin Tafsir, Sheikh Sulaimon Farooq Onikijipa ya rantse da Alkur'ani Mai Girma cewa ba shi da hanni a rashin lafiyar Sheikh Habeeb Adam (El-Ilory).

Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a jihar Kwara. 'Yan bindigan sun kashe shugaban kungiyar Miyetti Allah, bayan sun farmake shi a gaban gidansa.

Allah ya yi wa tsohuwar shugabar ma'aikatan gwamnatin jihar Kwara rasuwa, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya miƙa sakon ta'aziyya tare da addu'ar Alƙah jikanta.

Sanata Saliu Mustapha ya tallafa wa mutane 2,500 a Kwara, bayan ya horar da su kan sana’o’i don bunkasa kasuwanci, noma da rage fatara a Najeriya.

Kotun majistire mai zama a Ilorin, babban birnin jihar Kwara ta tasa keyar Abdulrahman Muhammed, wanda ya ce shi malamin musulunci ne zuwa gidan yari.
Kwara
Samu kari