
Kungiyar Izala







Marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir ya taba musuluntar da kabilar Cakobo baki daya, dukkan mutanen kabilar da sarkinsu. Malamin ya fara karatu wajen mahaifinsa.

Tsohon minista, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya tura sakon ta'azziya ga iyalai da yan uwan marigayi Sheikh Sa'idu Hassan Jingir da ya rasu a yau Alhamis.

Rasuwar Sheikh Saidu Hassan Jingir ta girgiza malamai da yan siyasa. Sheikh Daurawa, Isa Ali Pantami, gwamnoni da sauran yan siyasa sun yi ta'aziyya.

Mataimakin shugaban malaman kungiyar Izala Sheikh Saidu Hassan Jingir ya rasu bayan fama da jinya da ya yi. Malamin ya rasu a jihar Filato a azumi.

Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bude sabon masallaci a jihar Bauchi. Sheikh Guruntum zai fara tafsiri a masallacin.

Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya ambaci wasu ayyukan alheri da ya kamata kowane Musulmi ya yi a Ramadan. Ya ambaci Karatun Kur'ani, ciyar da mai azumi.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce DSS ta kama mai damfara da sunan Izala da Sheikh Kabiru Gombe bayan shafe shekaru yana cutar mutane a jihar Legas.

Sheikh Muhammad Bin Usman zai koma limanci a masallacin Kundila na Sahaba bayan rikici da aka yi a masallacin Jami'urrahma. Sheikh Ibrahim Kalil ne ya sanar da haka.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce a yanzu haka malamai sun kore su a siyasa sun fara yakin neman zabe suna nuna wanda ya kamata a zaba.
Kungiyar Izala
Samu kari