Zaben jihohi
Bola Tinubu ya taya Adeleke murnar lashe zaɓen Osun, ya bukace shi da haɗa kan jama’a, yayin da ya yaba wa INEC da jami’an tsaro kan zaɓe mai inganci.
Mawaki Davido ya gargadi Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, bayan nasarar Adeleke a Osun, yana mai cewa ya shirya domin mayar masa da martani kan kalamansa.
James Faleke ya musanta zargin Davido na cewa ya matsa wa hukumar INEC lamba kan sakamakon zaben Osun, inda ya ce ya je jihar ne domin tallafa wa APC.
Rabiu Kwankwaso ya taya Ademola Adeleke murnar lashe zaɓen Osun, ya yaba wa masu zaɓe da INEC, tare da kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaɓe mai gaskiya.
An lakada wa ɗan jaridar TheCable duka a rumfar zaɓen ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji yayin zaɓen jihar Osun, kafin ’yan sanda su shiga tsakani su kare shi.
Atiku Abubakar ya taya Ademola Adeleke murnar sake lashe zaɓen gwamnan Osun, bayan INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara da ƙuri’u 511,067.
Gwamna Ademola Adeleke na Accord ya lashe kananan hukumomi 19 a zaben jihar Osun, yayin da Bola Oyebamiji na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11.
Jigon Accord, Pelumi Olajengbesi, ya ce Tinubu ya taya Adeleke murnar nasarar zaben Osun kafin sanar da sakamakon, yana yaba wa shugaban kasar kan rashin tsoma baki.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar da dan takarar da ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Osun. Gwamna Ademola Adeleke ya samu tazarce.
Zaben jihohi
Samu kari