Labaran garkuwa da mutane
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kungiyar NURTW a jihar Kaduna. Miyagun sun sake sace shi ne bayan ya yi kwanaki 60 a hannunsu.
Tsohon dan majalisar wakilai, Sani Takori, ya bukaci gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal da ya hada kai da gwamnatin tarayya domin magance matsalar tsaro.
A wannan labarin, za ku ji dakarun sojan kasar nan sun fatattaki yan ta'adda a sassa daban-daban na kasar nan tare da hallaka takwas daga cikinsu.
Dakarun sojojin Najeriya da ke aikin samar da tsaro a jihar Taraba sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Taraba.
Rahotanni daga jihar Anambra a Kudu maso Gabashin Najeriya sun nuna wasu miyagu sun sace shugaban kauyen Abatete, High Chief Ezebinobi Ezeigbo ranar Talata.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki coci guda biyu a yankin ƙaramar hukumar Kajuru a Kaduna, sun hallaka mutane 3 tare da sace wasu akalla 30 ranar Lahadi.
Wasu matasa sun babbaka gawarwakin wasu da ake zargi yan bindiga ne a jihar Kaduna a Arewacin Najeriya. Sojoji sun kai farmaki ne kan yan bindigar ranar Laraba
Yan bindiga sun harbe mai hotel da manajansa da sauran mutanen da suka kama a hotel bayan sun kama su da daddare. Yan bindigar sun karbi kudin fansa kafin kisar.
Ta’adin Halilu Sabubu Buzu ya zo karshe domin sojoji sun hallaka shi, tun a watannin baya aka ji jami’an tsaro su na cigiyar Halilu Buzu domin a kashe shi.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari